Home Coronavirus Rigakafin Covid-19 ya kusa iso wa Nijeriya – PTF

Rigakafin Covid-19 ya kusa iso wa Nijeriya – PTF

28
0

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin shugaban kasa kan cutar Coronavirus, Boss Mustapha, ya ce shirye-shirye sun yi nisa a kokarin da ake na siyo allurar rigakafin cutar COVID-19 ga ‘yan Nijeriya.

Hakama ya bada tabbacin cewa, gwamnati za ta ci gaba da tabbatar da cewa allurar ba za ta zama barazana ga ‘yan Nijeriya ba idan aka siyo ta.

Mustapha ya bada wannan tabbacin a jiya Litinin a babban Birnin tarayya Abuja wajen bada bayanai na kwamitin.

DCL Hausa ta rawaito cewa, shugaba Buhari ya bada damar fadada matakan da ake dauka na hana yaduwar cutar a kasar, da suka hada da kayyade yawan ma’aikatan da za su rika zuwa aiki daga mataki na 12 zuwa sama.

Ya ce, kwamitin ya samu rahoton cewa akwai ma’aikatu da hukumomi da ke tilasta wa ma’aikatan da aka hana zuwa aikin, su dawo aiki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply