An harbi wani mutum mai suna Onyinye Onwuka mai shekaru 30 ya mutu har lahira biyo bayan wani musayar yawu kan wani fili a karamar hukumar Oshimili jihar Delta.
Jaridar Punch ta rawaito cewa har yanzu ba a ga wadanda suka yi harbin ba.
Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa wasu matasa ne suka yi harbin a lokacin da hayaniyar ta barke a tsakani kan filin.
