Hukumar kashe gobara ta Nijeriya reshen jihar Kano, ta ce wani yaro ɗan kimanin shekaru bakwai, da aka bayyana sunansa da Umar Ado, ya mutu sanadiyar faɗa wa wata rijiya a Unguwa Uku layin Yarabawa da ke ƙaramar hukumar Tarauni ta jihar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hudɗa da jama’a na hukumar, Alhaji Saidu Mohammed ya fitar a ranar Laraba.
Mohammed ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN, cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata yayin da yaron ya je ɗibar ruwa a rijiyar.
Ya ce “bayan an ciro gawar yaron daga cikin rijiyar sai aka garzaya da shi zuwa asibitin koyar wa na Murtala Muhammad, da ke Kano, inda anan ne aka tabbatar da mutuwarsa”.
