A yammacin ranar Laraba ne gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bakin kanar Bubakar Hasan ta yi karin haske kan harin ta’addanci da wasu ‘yan ta’adda suka kai ma wani barikin sojin garin Inates da ke cikin jihar Tillaberi mai iyaka da kasar Mali
Kanar Bubakar Hasan ya yi wannan bayani ne ta kafar talabajin din kasar ta Nijar inda ya bayyana cewa a yayin harin da daruruwan ‘yan ta’addar da suka shigo daga kasar Mali suka kawo sun kashe sojojin kasar kimanin 71 yayin da wasu 12 suka jikkata.

Sai dai gwamnatin ba ta yi wani karin haske ba kan adadin ‘yan ta’addar da aka kashe amma wata majiya ta daban na cewa ‘yan ta’addar 57 ne suka rasu a yayin gumurzun da aka share tsawan sa’o’i 3 ana kafsawa.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake kai ma wannan barikin Inates hari inda ko a karshen watan Yunin wannan shekara an kai ma wannan sansani hari, harin da ya yi sanadiyar rasa ran sojoji 18

A sakamakon haka ne ma shugaba Isufu Mahamadu da ke halartar wani taro kan zaman lafiya a kasar Masar ya katse ya dawo gida dan zama da lalubo mafita kan matsalar tsaron.
