Dan wasan kwallon kafa dan asalin kasar Portugal Cristiano Ronaldo, ya zama mutum na farko da ya samu adadin mabiya da yawansu ya kai milyan 251 a shafinsa na Instagram.
Shafin zada zumunta na Facebook na Goal.com ne ya bayyana haka a Litinin din nan.
Sai dan wasan Argentina Lionel Messi nada yawan mabiya a shafin nasa na Instagram da yawansu ya kai milyan 174.
Ko hakan na nuna cewa Ronaldo ya fi Messi magoya baya a duniyar tamaula?
