An samu rudani a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa a ranar Larabar nan, bayan da mataimakin sakataren jam’iyyar Victor Giodom ya bayyanna kan sa a matsayin mukaddashin shugaban jam’iyyar.
Wannan sanarwa na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da sakataren yada labaran jam’iyyar Lanre Issa-Onilu ya sanar da nada mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Kudu Abiola Ajimobi a matsayin mukaddashin shugaban jam’iyyar bayan dakatar da Adams Oshimole.
Da yake magana a wajen wani taron ‘yan jarida a sakatariyar jam’iyyar, Giodom ya fake ne da hukuncin da Alkali S. U. Bature ya yanke kan matsalar a ranar 16 ga watan Maris.
