Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Rufe iyakoki: An ƙwace kayan ₦11bn cikin shekara guda a Nijeriya

Rufe iyakoki: An ƙwace kayan ₦11bn cikin shekara guda a Nijeriya

211
0

Rundunar haɗin guiwa da ke tsaron iyakokin Nijeriya ta ce ta ƙwace kayan da kuɗinsu ya kai Naira Biliyan ₦11 a cikin shekara guda.

Mai magana da yawun rundunar Joseph Attah ya bayyana haka a cikin wata sanarwar cika shekara guda da fara aikin rundunar da ya fitar a Abuja, ranar Talata.

Ita dai wannan runduna da ta ƙunshi hukumar hana fasa ƙwabri, hukumar shige da fice, rundunar soji da ta ƴan sandan Nijeriya da kuma sauran hukumomin tsaro da leƙen asiri ta fara aikinta ne a ranar 20 ga watan Agustan 2019 ƙarƙashin kulawar ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro.

Attah ya yi bayanin cewa daga cikin kayan da aka kama, akwai buhu 134,042 na shinkafa, buhun taki 9,600 na NPK, motoci 1,791, litar man fetur miliyan 3,565,461.9 da diram 5,007 shaƙare da man fetur da dai sauransu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply