Home Labarai Rufe iyakokin Nijeriya: WACTAF ta koka, ta nemi daukin ECOWAS

Rufe iyakokin Nijeriya: WACTAF ta koka, ta nemi daukin ECOWAS

75
0

Kungiyar ‘yan kasuwar kasa da kasa, karkashin jagorancin kungiyar ‘yan kasuwar kayan gona da kifi na Afrika ta yamma WACTAF sun yi kira ga kungiyar ECOWAS ta sa baki ga rufe kan iyakokin da Nijeriya ta yin a tsawon lokaci.

 

A cikin wata takarda da kungiyar ta aikewa shugaban ECOWAS mai dauke da ranar 8 ga watan Fubrairu, 2020, ta ce rufe iyakokin ya jefa ‘ya’yan ta cikin mawuyacin hali inda wasu ma suka bar kasuwar sama da watanni shida kenan.

Takardar, wadda ta samu sa hannun sakataren kungiyar na biyu Salami Alasoadua, ta yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta dauki dukkan matakan da suka dace na saki wasu tirelolin kaya da aka kama a kan iyakokin, domin kuwa akwai kayan da za su iya lalacewa a ciki.

Da take kira ga Nijeriya ta janye matakin rufe iyakokin, kungiyar ta c eta kafa kwamiti da zai tallafawa kokarin gwamnatin kasar wajen magance matsalolin da take fuskanta da sauran kasashen ECOWAS musamman Jamhuriyar Nijar da Benin.

Saidai kuma ministan noma da raya karkara na Nijeriya Sabo Nanono ya yi bayanin cewa rufe iyakokin na wucin gadi ne, da zia taimakawa kasar shawo kan wasu matsaloli da take fuskanta na tattalin arziki da ci gaban rayuwar jama’ar kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply