Home Labarai Rufe makarantu ba shi ne mafita ga Covid-19 ba – Ganduje

Rufe makarantu ba shi ne mafita ga Covid-19 ba – Ganduje

40
0

Gwamnatin jihar Kano ta ce sake rufe makarantu a daidai lokacin da cutar Covid-19 ta yi kome, ba zai haifar da komai ba sai sake maida al’umma baya.

Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka a lokacin wani taron wayar da kai na masu ruwa da tsaki a ɓangaren ilimi kan Covid-19, wanda ya gudana a gidan gwamnatin Kano ranar Juma’a.

Ganduje, ya ce duk da kasancewar akwai matuƙar buƙatar yaƙar cutar, amma duk da haka yana da kyau a riƙa taka tsantsan wajen kaucewa illar da matakan da ake ɗauka za su iya haifarwa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply