Home Labarai Ruftawar daki ta hallaka uba da ‘ya’yansa a Katsina

Ruftawar daki ta hallaka uba da ‘ya’yansa a Katsina

407
1

Rugujewar daki ta yi sanadiyyar mutuwar mutane uku a Unguwar Tsamiya karamar hukumar Dutsinma, jihar Katsina.

Dakin ya rufta ne bayan wani mamakon ruwan sama a yankin na karamar hukumar Dutsinma.

Mutumin mai suna Malam Mai Shanu, “masinja” ne a kotun shari’a da ke Dutsinma, in da rahotanni suka ce matar maigidan ce kawai ta tsira da ranta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

Leave a Reply