Home Sabon Labari Ruga: Shugaban kwamitin amintattu na PDP ya goyi bayan shirin RUGA

Ruga: Shugaban kwamitin amintattu na PDP ya goyi bayan shirin RUGA

60
0

Daga Nuruddeen Ishaq Banye.

Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP Sanata Walid Jibrin ya yi kira ga ‘ƴan Nijeriya da su goyi bayan shirin gwamnatin tarayya na ƙirƙiro da filayen kiwon dabbobi na zamani.

Da yake ganawa da manema labarai a gidansa da ke jihar Nasarawa jiya Talata, Jibrin ya ce shirin na RUGA, zai taimaka wajen kawo zaman lafiya da ci gaban tsaro a ƙasar.

Ya kuma yi bayanin cewa shirin, zai taimaka wajen wadatar abinci da kiwon lafiya da kuma kyautata rayuwar al’umomin yankunan karkara.

A kan haka, Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar ta PDP, ya yaba wa gwamnatin tarayya kan ɓullo da shirin, sannan ya yi kira ga sauran ƙabilun Yarabawa da Ibo, da su ma su goyi bayan shirin domin ci gaban ƙasa.

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ce dai ta yi yunkurin bullo da sabon tsarin kiwon dabbobi a zamanance domin rage ko kawar da tada hatsaniya da ake samu tsakanin makiyaya da manoma.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply