Home Labarai Rundunar ƴansandan Kebbi ta yi sabon Kwamishina

Rundunar ƴansandan Kebbi ta yi sabon Kwamishina

35
0

Rundunar ‘yansandan jihar Kebbi ta sanar da isowar sabon kwamishinanta Adeleke Adeyinka Bode.

Kakakin Rundunar DSP Nafi’u Abubakar ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da DCL Hausa ta samu a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce sabon kwamishinan wanda ya maye gurbin AIG Agubiade Oluyemi Lasore da ya samu karin matsayin zuwa mataimakin Sifetan ‘yansanda, ya fara aiki ne nan take.

Adeyinka Bode, wanda dan asalin karamar hukumar Ekiti ne daga jihar Kwara, ya shiga aikin dansanda ne a ranar 3 ga watan Maris na shekarar 1990 a matsayin ASP.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply