Home Labarai Rundunar “Operation Sahel Sanity” ta kashe ‘yan ta’adda, ta ceto matan da...

Rundunar “Operation Sahel Sanity” ta kashe ‘yan ta’adda, ta ceto matan da aka sata a Katsina

88
0

Rundunar tsaro ta musamman mai lakabin “Operation Sahel Sanity” da ke da matsuguni a Faskari jihar Katsina ta ce ta kashe wani da ake zargin dan ta’adda ne a samamen da take kai wa don dakike ayyukan ta’addanci.

Rundunar ta musamman ta kuma gano bindiga samfurin AK47 shakare da alburusai.

Mukaddashin daraktan watsa labarai na rundunar Brig Gen Bernard Onyeuko ne ya tabbatar da hakan a cikin takardar da ya raba wa manema labarai a Katsina.

Takardar ta ce sojojin sun durfafi ‘yan ta’addar da ke labe cikin gezoji, da hakan ya yi sanadiyyar raunata da dama daga cikinsu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply