Home Labarai Rundunar sojin Nijeriya ta hallaka ƴanta’adda 108 cikin mako ɗaya

Rundunar sojin Nijeriya ta hallaka ƴanta’adda 108 cikin mako ɗaya

161
0

Shelkwatar tsaron Nijeriya ta ce daga ranar Alhamis ta makon jiya zuwa makon nan, jami’an sojojinta sun kashe ƴanta’adda akalla 108 a yankin Arewa maso yamma da kuma ƴanta’adda da dama a yankin Arewa maso Gabas.

Jami’in yada labarai na rundunar Manjo-Janar John Enenche ne ya sanar da haka a Abuja yayin taron mako-mako na ayyukan sojin kasar.

Enenche ya ce a makon jiya kadai dakarun sojojin da ke atisayen ‘Operation Hadarin Daji sun kai hare-hare a mafakar ƴanta’addan tare da yin gagarumar nasara a jihohin Sokoto, Katsina, Kano, Jigawa, Zamfara, Kebbi da kuma Kaduna.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply