Home Labarai Rundunar sojin Nijeriya ta sha alwashin kawar da matsalar rashin tsaro

Rundunar sojin Nijeriya ta sha alwashin kawar da matsalar rashin tsaro

286
0

Babban Hafsan Sojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya ce sojojin Nijeriya za su ci gaba da lalubo sabbin hanyoyin dakile duk wata hanya da ke kawo barazanar tsaro a fadin kasar.

Buratai ya bayyana hakan ne a wani taron karawa juna sani tare da jami’an yaɗa labarai na kwanaki hudu mai taken: “Tallafawa Sojoji don samar da tsaron Kasa,” wanda aka fara a Legas a ranar Litinin.

Buratai wanda ya samu wakilcin Manjo Janar Godwin Umelo, babban kwamandan rundunar (GOC), shiyya ta 81, ya ce taron hadakar zai haifar da nasarori da kawo gagarumin sauyi wajen kara inganta hanyoyin samar da tsaro a fadin kasar nan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply