Home Sabon Labari Ruwan Sha A Gidan Soja:  Sojoji za su gina ma’danar ruwa mai...

Ruwan Sha A Gidan Soja:  Sojoji za su gina ma’danar ruwa mai cin lita Milyan Daya a rana.

118
0

Daga Abdullahi Garba Jani

 

Domin tabbatar da tsafta da ingancin ruwan sha a barikoki da sauran matsugunan jami’an soji, rundunar sojin kasa ta Nijeriya za ta gina ma’danar ruwa mai cin lita Milyan Daya a duk rana a Maxwell Khobe Cantonment dake Rukuba, kusa da birnin Jos, jihar Plateau.

 

Babban hafsan sojin Nijeriya Lt. Gen. Tukur Buratai ya furta hakan a lokacin da ya ke dora harsashin ginin ma’adanar ruwan a Rukuba.

 

Buratai da ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya -NAN-, ya ce rundunar sojin ta dauki wannan matakin ne don rage bazuwar cutuka a tsakanin jami’an sojin Nijeriya, ta dalilin karancin ruwan sha.

 

Cutuka da dama na yawan bazuwa a tsakanin mutane, ta dalilin tu’ammali da gurabataccen ruwan sha. Sai dai gwamnatoci a matakai daban-daban, na ta shelar cewa suna kokarin samar da ruwan sha tsaftatacce kuma isasshe.

Wasu sojin Nijeriya a bakin aiki

Masu sharhi kan lamurran yau da kullum na ganin kamar ana fakewa da “guzuma” don a harbi “karsana” ta yadda ake zargin fitar da kudin aikin samar da ruwan a lokuta daban-daban, amma kwalliya ba ta biyan kudin sabulu.

 

Domin tabbatar da samar da wadatacce kuma tsaftataccen ruwan sha a duniya, Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 22 ga watan Maris na kowace shekara don ingantawa tare da yekuwar Samar da ruwan sha a tsakanin al’umma kuma irin wannan kokari da rudunar sojin  kasa ta ce ta yi a jihar filato na cikin abubuwan da ake duba wurin auna ci gaba ko akasin haka a bangaren samar da tuwan sha.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply