Home Sabon Labari Sabbin Masarautun Kano: Kotu ta ce Ganduje ya dakata-Taskar Guibi 11.12.2019

Sabbin Masarautun Kano: Kotu ta ce Ganduje ya dakata-Taskar Guibi 11.12.2019

70
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, goma sha hudu ga watan Rabiul/Rabiyul Sani, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha daya ga watan Disamba, na 2019.

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike wa Majalisar Dattawa wasikar neman amincewarta ya nada Muhamnad Nami a matsayin sabon shugaban hukumar tara kudaden shiga na cikin gida FIRS.

2. Majalisar Wakilai za ta gudanar da bincike a kan kutsawa kotu da jami’an hukumar DSS suka yi domin kama Sowore.

3. Kotu ta dakatar da kaddamar da sabbin sarakuna hudu masu daraja ta daya da gwamnan jihar Kano Ganduje ya sake kirkirowa.

4. Farfesa Attahiru Jega ya nuna damuwarsa a game da Nijeriya ce a kan gaba a Afirka, bangaren karuwar rashawa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply