Home Labarai Sabbin Ministoci: Majalisar dattawa a Nijeriya ta amince da nadin ministoci 43.

Sabbin Ministoci: Majalisar dattawa a Nijeriya ta amince da nadin ministoci 43.

74
0

Daga Abdullahi Garba Jani

Majalisar dattawa a Nijeriya ta amince da sunaye 43 da shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ya aike ma ta don nada wa ministoci.

An dai fara shirin tantance sunayen ne a ranar Larabar makon jiya 24 Juli, 2019 da Mr Uchechukwu Ogah daga jihar Abia, Wanda aka kammala ranar Talata 30 Juli, 2019 da Alh Lai Muhammad daga jihar Kwara.

Bayan kammala shirin tantancewar ne, majalisar ta ci gaba da shirin tabbatar da su a matsayin ministoci.

Shirin tantancewar dai ya dauki majalisar dokokin Nijeriya har kwanaki 5.

Abin jira a gani dai shi ne, sauraron ba da ma’aikatu daga shugaba Buhari ga ministocin don kama aiki.

Ga dai jerin sunayen wadanda majalisar ta tantance kuma ta amince da su:

1. Uchechukwu Ogah (Abia)
2. Godswill Akpabio (Akwa Ibom)
3. George Akume (Benue)
4. Ogbonnaya Onu (Ebonyi)
5. Emeka. Nwajuaba (Imo)
6. Olorunnibe Mamora (Lagos)
7. Olamilekan Adegbite (Ogun)
8. Adamu. Adamu (Bauchi)
9. Rotimi Amaechi (Rivers)
10. Sharon Ikeazor (Anambra)
11. Tayo Alasoadura (Ondo)
12. Mustapha Shehuri (Borno)
13. Abubakar Aliyu (Yobe)
14. Bashir Magashi (Kano)
15. Ramatu Aliyu (Kogi)
16. Timipre Sylva (Bayelsa)
17. Zubairu Dada (Niger)
18. Chris Ngige (Anambra)
19. Abdullahi Hassan (Nasarawa)
20. Sunday Dare (Oyo)
21. Muhammad Bello (Adamawa)
22. Sadiya Farouq (Zamfara)
23. Zainab Ahmed (Kaduna)
24. Adeniyi Adebayo (Ekiti)
25. Abubakar Malami (Kebbi)
26. Hadi Sirika (Katsina)
27. Osagie Ehanire (Edo)
28. Paullen Tallen (Plateau)
29. Festus Keyamo (Delta)
30. Ali Isa Pantami (Gombe)
31. Maigari Dingyadi (Sokoto)
32. Babatunde Raji Fashola (Lagos)
33. Dr.Mohammed Mahmoud (Kaduna)
34. Gbemisola Saraki (Kwara)
35. Rauf Aregbesola. (Osun)
36. Goddy Jedy- Agba (Cross River)
37. Suleiman Adamu Kazaure (Jigawa)
38. Amb Mariam Katagum (Bauchi)
39. Clement I.K. Anade Agba (Edo)
40. Geoffrey Onyeama (Enugu)
41. Engr. Saleh Mamman (Taraba)
42. Sabo Nanono (Kano)
43. Lai Mohammed (Kwara)

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply