Home Sabon Labari Sabbin Sarakunan Kano sun ziyarci Ganduje don tayasa murnar nasara a Kotu

Sabbin Sarakunan Kano sun ziyarci Ganduje don tayasa murnar nasara a Kotu

69
0

Sabbin sarakuna na jihar Kano guda 4 da Gwamna Ganduje ya nada a shekarar da ta gabata sun kai masa ziyarar taya murnar cin nasara a kotun koli a ranar Litinin din nan. Sarakunan na Gaya da Bichi da Rano da Karaye sun gana da Gwamnan  a Africa House wato gidan gwamnatin jihar Kano, acewar sanarwar da Abba Anwar Babban Mai Magana da yawun Gwamnan ya fitar.

Sanarwar ta ce a sakamakon yawan jama’ar da Sarakunan suka shigo da su gidan gwamnati, dole aka ware wa kowannensu akalla mintuna 30 don da shi da jama’arsa su gana da Gwamna Ganduje. Abba Anwar ya ce Sarakunan sun taya Gwamna Ganduje murnar nasarar da ya samu daga shari’ar zabe da jam’iyyar adawa ta PDP ta shigar. Ya ce Sarakunan sun godewa Gwamnan a kan ayyukan raya kasa da yake shimfidawa a fadin jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya ji dadin wannan ziyara kuma ya ce ya gode musu. Gwamnan ya ce yana sane da irin addu’o’in da sabbin Sarakunan da jama’arsu suka rinka yi domin ganin ya yi nasara a kotun koli. Ya ce yana fata yanzu Sarakunan za su ci gaba da bada gudunmawa wurin ci gaban jihar Kano.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply