Hukumar zaɓe ta Nijeriya INEC ta bayyana Rotimi Akeredolu a matsayin ɗan takarar da ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Ondo.
Mr Akeredolu ya samu kuri’a 292,830, ya yin da dantakarar jam’iyyar PDP, Mr Eyitayo Jegede ya ke biye masa da kuri’a 195,791, sai kuma dan takarar ZLP, Agboola Ajayi, wanda ya samu kuri’a 69,127.
Dukkanin ‘yan takarar uku lauyoyi ne kuma sun fito daga mazaɓun sanata uku daban-daban – Akeredolu daga Ondo ta Arewa; Jegede daga Ondo ta Tsakiya da kuma Ajayi daga Ondo ta Kudu.
Mista Akeredolu ne gwamnan da ke kan mulki a jihar tun shekarar 2016.
