Home Sabon Labari SABON LABARI:’Yan sandan Katsina sun kwato ɗaliban Islamiyya 84 da aka sace

SABON LABARI:’Yan sandan Katsina sun kwato ɗaliban Islamiyya 84 da aka sace

1335
0

Rahotannin da DCL Hausa ke samu bada jimawa ba na cewa ‘yan sanda a Katsina sun kwato dalibai 84 da aka yi garkuwa da su a ranar Asabar da daddare.

Kakakin’yan sandan a Katsina SP Gambo Isa ya ce tun a lokacin da abin ya faru ‘yan sanda suka bi ‘yan bindigar su kuma kwato daliban su 84 na Islamiyyar Hizburrahim da ke Mahuta Dandume. Isa ya ce yanzu haka a wayewar garin Lahadin nan ‘yan sanda na duba inda aka yi artabun ko za su samu ‘yan bindigar da suka ji rauni domin a artabunsu na Asabar da daddare jami’an tsaro sun yi fata fata da ‘yan bindigar.

DA DUMI-DUMI: Ana zullumin an yi garkuwa da daliban Islamiyya masu yawa a Dandume, Katsina

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply