Home Labarai Sabuwar shekara – El-Rufai ya yi afuwa ga ƴan gidan yari

Sabuwar shekara – El-Rufai ya yi afuwa ga ƴan gidan yari

101
0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya yi afuwa ga ƴan gidan yari 12 a jihar yayin bikin murnar sabuwar shekara a jiya.

Mai ba gwamnan shawara kan yada labarai Muyiwa Adekeye ya shaida cewa yin afuwar na bisa tsarin damar da kundin tsarin dokar kasar nan ya ba gwamnan a sashe na 212.

Cikin wadanda gwamnan ya yi wa afuwa sun hada da Gabriel Olugbenga dan shekara 60 wanda aka yankewa hukuncin zaman gidan na shekara 7 kuma saura wata 6 ya gama, sai Tunde Ikuenaya dan shekara 64 da aka yanke wa hukuncin zaman shekara 4, saura wata 3 ya gama wa’adin nasa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply