Home Labarai Sabuwar  shekarar musulunci:  Sarkin musulmi ya bukaci da a fara duba jinjirin...

Sabuwar  shekarar musulunci:  Sarkin musulmi ya bukaci da a fara duba jinjirin watan Muharram

96
0

Abdullahi Garba Jani/dkura

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci musulmin Nijeriya da su fara duba jinjirin watan Muharram na shekarar musulunci ta 1441 a ranar Juma’a 30 ga watan Agusta, 2019.

 

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya rawaito cewa ganin watan na Muharram ne zai alamta shigowar sabuwar shekarar musulunci ta 1441 A.H.

 

Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi wannan kiran ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin kula da harkokin addinin musulunci na masarautar Prof. Sambo Junaid a Sokoto.

 

 

Kazalika, Sarkin Musulmin ya bukaci mutane da su kai rahoton ganin sabon watan ga Dagaci ko Hakimin da ke kusa da su don aike wa da sakon gare shi.

 

Sai ya yi adu’ar Allah ya kara taimakon musulunci da al’ummar musulmi baki daya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply