Home Labarai Sadaukin Shinkafi: Femi Kayode yace babu al’ummar da ba mutanen kirki

Sadaukin Shinkafi: Femi Kayode yace babu al’ummar da ba mutanen kirki

623
0

A shafinsa na Facebook, Sadaukin Shinkafi Femi Fani-Kayode, ya ce ya yi mamaki kwarai da ya ga Sarkin Shinkafi ya nada shi wannan sarauta mai matukar tarihi. A don haka ya ce wannan zai karfafa masa gwiwa wurin kira ga ‘yan Nijeriya da a zo a zauna lafiya a kuma samar da hadin kai.

Ya ce an nuna mishi kauna a cikin kwanaki 7 da ya yi a Zamfara. Kazalika ya ce ya fahimci cewa babu wata al’umma da babu mutanen kirki da mutanen da bana kirki ba.

Ya jinjina wa Gwamnan Zamfara da ya ce shi ne ya assasa zuwansa jihar, kuma ya ji dadi sosai. Kazalika Femi Fani-Kayode ya ce ya ji dadin kalamai masu ratsa jiki da Sarkin Musulmi Alhaji Saad Abubakar ya yi a lokacin da ya kai ma Sarkin ziyara.

Sai dai Sadaukin Shinkafi wanda wasu mutanen arewacin Nijeriya suka nuna jin haushin basa wannan sarauta ya ce babu wani abu da zai sa ya sauya yadda yake kira da a yi adalci a Nijeriya ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply