Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Sifurin jirage: Filayen jirage 5 ne kacal za a fara budewa a...

Sifurin jirage: Filayen jirage 5 ne kacal za a fara budewa a Nijeriya – NCAA

102
0

Biyo bayan amincewa da sake dawo da harkar sufurin jiragen sama a Nijeriya daga ranar 21 ga watan Yuni, hukumar kula da sufurin saman Nijeriya ta amince da bude filayen jiragen sama guda biyar don faraway da su.

Babban Daraktan hukumar Captain Musa Nuhu ya bayyana haka a cikin wata takarda da ya aikewa shugabannin kamfanonin jiragen sama cikin gida da na waje.

Takardar ta ambaci filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Lagos, Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, babban filin jirgin Fatakwal, da na Omagwa a jihar Rivers, da na Malam Aminu Kano da ke Kano da kuma na Sam Mbakwe da ke Owerri a matsayin filayen jirage biyar da za a fara budewa.

Babban Daraktan ya kara da cewa duk wasu filayen jiragen sama da ba su cikin jerin wadannan biyar da ke son budewa, to wajibi ne sai sun cika sharuddan matakan yaki da cutar Covid-19.

Saidai kuma ya ce ba za a ci gaba da safarar jiragen saman zuwa kasashen waje ba, har sai zuwa lokacin da aka sanar da amincewar hakan, indai ba muhimmiyar safara, ko kuwa ta gaggawa ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply