Rundunar sojin Nijeriya ta yi kiran haɗin kai da sauran hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen ƴan bindiga da sauran masu aikata laifuka a Katsina da ma sauran yankin Arewa maso Yamma.
Mataimakin babban hafsan sojin ka bayanan sirri Manjo Janar Gbolahan Oyefesobi ya yi wannan kiran a ranar Laraba, lokacin da ya kai ziyarar aiki a sansanin sojoji na Faskari, da ke jihar Katsina.
Oyefesobi, ya ce duk cewa akwai fahimta tsakanin sojoji da sauran hukumomin tsaron, amma ƙara inganta alaƙar za ta taimaka wajen cimma nasara ga yaƙi da matsalar tsaron da ake yi.
