Home Labarai Sai da haɗin kan iyayen ƙasa tsaro zai inganta – Buhari

Sai da haɗin kan iyayen ƙasa tsaro zai inganta – Buhari

120
0

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a jiya Talata ya umurci gwamnoni da su kara hada kai tare da yin aiki da sarakunan gargajiya da sauran al’umma domin inganta hanyar tattara bayanan sirri na cikin gida don magance matsalolin tsaro da ke addabar kasar nan.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin ganawa da gwamnonin jihohin Nijeriya kan batun yadda za a magance matsalar tsaro a fadarsa da ke Abuja.

Buhari ya ce “tsaro yana da muhimmanci kuma dole ne mu tabbatar da an samar da tsaro a fadin kasa baki daya.

“Muna kuma yin tunani da dogon nazari sosai game da batun satar mutane don biyan kudin fansa”. in ji shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply