Home Labarai Sai kowa ya gyara halin sa za a samu tsaro – Masari

Sai kowa ya gyara halin sa za a samu tsaro – Masari

151
0

Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya ce dole ne sai jama’a sun sauya ɗabi’unsu idan har ana so a kawo karshen matsalar kashe-karshen da ake.

Masari ya bayyana haka a ranar Alhamis, lokacin rufe yaƙin neman zaɓen ɗan takarar jam’iyyar APC, a zaɓen cike gurbin ɗan majalisar jihar, wanda ya gudana a Kabomo cikin ƙaramar hukumar Bakori.

Masari ya ce tuni mutane suka bar hanyar Allah, kuma har yanzu kowa yaƙi ya hankalta duk da irin isharorin da ake gani na sakamakon munanan ayyukan da jama’a ke aikata wa.

Ya ce idan har ana son zama lafiya, to wajibi ne a koma ga Allah tare da neman gafararsa da kuma roƙon ya kawo sauƙi kan halin da ake ciki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply