Home Labarai Sai kowa ya kawo dauki don yakar ta’addanci – Zulum

Sai kowa ya kawo dauki don yakar ta’addanci – Zulum

121
0

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya nemi da a hada guiwa tsakanin bangaren gwamnatin jihar dama na majalisar kasar nan wajen hana kungiyar ‘yan ta’adda daukar matasa suna saka su a cikin kungiyoyinsu.

Gwamna Zulum ya bayyana haka ya yin da kwamitin majalisar dattawa kan ayyuka na musamman karkashin jagorancin shugaban kwamitin Sanata Yusuf Yusuf ya kai musu ziyara a yankin arewa maso gabas.

Ya kuma yi kira ga hukumar raya yankin arewa maso gabas ta bayar da gudunmawar motoci guda dari ga ‘yansanda domin yakar masu harin ta’addanci.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kwamitin Sanata Yusuf Yusuf, ya yi alkawarin za a kara yawan kasafin kudin da ake ba jihohin yankin arewa maso gabas din da rikicin ta’addanci ya yi wa illa, domin su samu su farfado.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply