Home Coronavirus Sai yanzu tallafin corona ya isa Jigawa

Sai yanzu tallafin corona ya isa Jigawa

207
1

Gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da cewa ta karbi motoci guda dari makare da buhunan hatsi wanda gwamnatin tarayya ta aiko domin a raba a matsayin tallafin corona.

Gwamna Badaru Abubakar ne ya sanar da haka ga manema labarai a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse.

Gwamnan ya kara da cewa kowace mazaba da ke fadin jihar za a bata tan daya na hatsin domin a taimakawa al’ummar jihar.

Daga karshe gwamnan ya bayyana cewa sun sami tallafin kudi kimanin naira milyan dubu daya daga gwamnatin ta tarayya sai kuma karin wasu kayayyaki daga kungiyoyi daban-daban masu zaman kan su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

Leave a Reply