Home Sabon Labari Sakamakon wasannin firimiyar Nijeriya mako na farko

Sakamakon wasannin firimiyar Nijeriya mako na farko

87
0

Bayan shafe kimanin watanni 10, a ranar Lahadin nan aka dawo buga gasar Firimiyar Nijeriya inda aka buga wasanni a sassa daban daban na ƙasar, da suka zo da sakamako na ba zata.

Masu riƙe da kambun gasar Plateau United, sun fara da ƙafar hagu, inda suka yi rashin nasara a gida da ci 2-0 hannun Kwara United da suka sha da ƙyar a kakar bara.

MFM kuwa ta yi nasara ne kan Warri Wolves da ci 2-1 a wasan da aka buga a filin wasa na Agege, jihar Lagos.

Jigawa Golden Stars ta doke Sunshine Stars 1-0 a wasan da suka buga a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna.

A birnin Lafiya kuwa, Nasarawa United ta doke Wikki Tourist da ci 2-1 sai wasan da aka tashi kunnen doki 1-1 tsakanin Adamawa United da Kano Pillars a Birnin Yola.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply