Home Sabon Labari Sakataren Gwamnatin Katsina ya hori matasa su rungumi sana’o’in hannu

Sakataren Gwamnatin Katsina ya hori matasa su rungumi sana’o’in hannu

60
0

Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Muhammad Inuwa ya hori matasa da su riki sana’a da muhimmanci don kare mutuncinsu da bada gudunmuwa ga ci gaban al’umma.

Dr Mustapha Inuwa ya bada shawarar hakan ne jim kadan bayan an rantsar da shugabannin riko na mazabu na Jam’iyyar APC reshen karamar hukumar Danmusa.

Ya ce a matsayin su na matasa, wajibi ne a nan ragamar tafiyar da harkokin gwamnati da saran alamurran jama’a su komo kan su.

Saboda haka ya ce wajibi ne ga duk mai son a dama da shi idan lokacin ya yi, ya dage ga neman ilimi da kuma kama sana’a kome kankantar ta.

Ya kuma bukaci wadanda aka rantsar da sauran yansiyasa da su rika mutunta jama’a tare da yi masu bayani akan yanayin da jamiyya da gwamnati take ciki.

Akan yanayin tabarbarewar tsaro kuwa, Sakataren Gwamnatin ya bukaci al’umma da a dage ga yin addu’o’in neman Allah ya kawo karshen al’amarin.

Mustapha Inuwa ya kuma bukaci jama’a da su kai rahoton duk wanda suka ga yan take taken shi ba abin yarda ba ne.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply