Gwamnatin tarayya ta ce ba za ta iya bude makarantu ba a halin yanzu har sai komai ya daidaita.
Karamin Ministan Ilimi Chukwuemeka Nwajiuba ya fadi haka a Abuja da daren ranar Litinin lokacin jawabin kwamitin shugaban kasa na yaki da Covid-19.
Ministan ya karyata rahotanni da ake yadawa na cewa gwamnati za ta bude makarantun a ranar 21 ga watan Yuni.
Ya ce babu yadda za a bude makaranta a halin yanzu har sai masana a fannin lafiya sun bada damar hakan.
saidai ya ce abun da suke kokarin yi a halin yanzu shi ne kawo masu kammala karamar sakandire da kuma zana jarabawar WAEC domin su yi jarabawar su.
