Home Labarai Sakkwatawa na ko-oho ga rijistar katin dan kasa – NIMC

Sakkwatawa na ko-oho ga rijistar katin dan kasa – NIMC

304
0

A jihar Sakkwato, hukumomin da ke kula da rijistar katin dan kasa na cigaba da kokawa inda suke korafin har yanzu fa kashi goma Sha shidda ne 16% ne kacal na al’ummar jihar suka yi rijistar katin inda kashi 74% sunyi kememe sun ki yin rijistar.

Engineer Garba Balarabe ne shugaban hukumar samar da Katin dan kasa a Jihar Sakkwato ya ce sun saukaka aikin inda suka fadada aikin wajen samar da cibiyoyi har yankunan karkara, amma har yanzu aikin na tafiyar hawainiya, amma sun ce kara kulla dangantaka da hukumar wayar da kai ta kasa NOA zai taimaka.

Yin rijistar katin dan kasar zai taimaka sosai ga shawo kan rashin tsaro da kasar nan ke fuskanta, domin ko da zarar ka yi ta, akwai dukkanin bayanan ka a ciki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply