Home Labarai Sama da ƴan gudun hijira 2000 sun koma gidajensu a Katsina

Sama da ƴan gudun hijira 2000 sun koma gidajensu a Katsina

184
0

Kimanin ƴan gudun hijira 2,027 ne waɗanda hare-haren ƴan bindiga ya sa suka bar ƙauyukansu a makon jiya, suka koma gidajensu ranar Litinin, a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Mutanen da suka fito daga ƙauyukan Tsamben Tsauni, Tsamben Kotumbo, Tsamben Raɗi da Tsamben Zango, sun baro gidajensu ne tare da yada zango a makarantar firame ta garin Jibia a ranar Alhamis bayan ƴan bindiga sun riƙa kai masu hari a ranakun Talata da Larabar da ta gabata.

A cewar Magaji Tsamben Tsauni Ibrahim Ali, ƴan bindigar sun yi wa mata da yawa fyaɗe tare da raunata mazajen da suka ƙi basu kuɗi.

Gwamnatin jihar Katsina ce dai ta jagoranci mayar da mutanen ƙauyukansu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply