Home Labarai Sama da ƴan Nijeriya miliyan biyu suka rasa muhallansu

Sama da ƴan Nijeriya miliyan biyu suka rasa muhallansu

107
0

Ministar agaji da kare aukuwar ibtila’i ta Nijeriya Sadiya Umar Farouk, ta ce yanzu haka kasar na da yawan mutane sama da miliyan biyu da suka rabu da muhallansu.

Ta ce wadanda abun ya shafa sun rasa muhallan nasu ne ta sanadiyyar ayyukan ta’addanci da ‘yanbindiga ko kuma rikicin kabilanci.

Ministar ta fadi haka ne a lokacin da take ganawa da ‘yanjaridar fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, bayan wata ganawa da ta yi da shugaba Buhari a Abuja.

Sadiya, ta ce ta kawo wa shugaba Buhari ziyara ne domin ta gode masa kan irin goyon bayan da yake badawa kan batutuwan da suka shafi masu nakasa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply