Home Labarai Sama da ɗalibai 24,000 ba su koma makaranta ba a Lagos

Sama da ɗalibai 24,000 ba su koma makaranta ba a Lagos

37
0

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ya ce sama da yara 24,000 ne har yanzu ba su koma makaranta ba a jihar, tun bayan dokar kulle ta farko da aka yi sakamakon yaduwar cutar coronavirus.

gwamnan wanda ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da ‘yanjarida a gidan gwamnatin jihar, ranar Talata, ya ce daya daga cikin dalilin sake bude makarantun jihar shi ne don kare yaran daga fadawa halin yaruwa da ya hada da rashin zuwa makaranta baki daya.

Ya ce yanzu haka adadin yaran da ba su zuwa makarantar, iyayensu ne ko masu kula da su ne suka juyar da su zuwa wasu abubuwan, maimakon kyale su su koma makaranta don samun ilimi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply