Home Labarai Samar da tsaro hakƙin kowa ne – Masari

Samar da tsaro hakƙin kowa ne – Masari

155
0

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya ce yaƙi da ƴan bindiga da sauran matsalolin tsaro, hakƙi ne da ya wajjaba a kan kowa don ceto Nijeriya.

Gwamnan ya faɗi haka ne a ranar Alhamis, lokacin da shugabannin gudanarwar kamfanin Media Trust masu Jaridar Daily Trust suka kai masa ziyara a Katsina.

Ya ce a ɓangaren kafafen yaɗa labarai, duk da dai sun fi son labari marar daɗi, amma ya ce duk da haka, ya kamata su mayar da hankali wajen bada labaran irin nasarorin sa ake samu a ɓangaren tsaron ba wai labarun da za su karya wa jama’a zuciya ba.

Ya ƙara da cewa wajibi ne ga dukkan masu ruwa da tsaki su yi duba ga abubuwan da suke yi ba daidai ba, da manufar kawo gyaran da komai zai daidaita.

A jawabin sa tun da farko, muƙaddashin shugaban kamfanin Media Trust Mallam Nura Daura, ya ce sun zo Katsina ne don ƙarfafa alaƙar da ke tsakaninsu da kuma gabatar da sabbin shugabannin gudanarwar kamfanin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply