Cibiyar kimiyar kiwon Dabbobi ta Nijeriya ta ce za ta iya mayar da sana’ar kiwo a matsayin babbar hanyar samar da kuɗin shiga ga ƙasar, ta hanyar amfani da fasaha da ƙirƙiren zamani.
Shugaban Cibiyar Farfesa Eustace Ajayi ya faɗi haka a lokacin wani taron ƴan Jarida kan babban taron shekara da Cibiyar za ta yi a Abuja cikin watan nan, mai taken ‘Muhummacin fasahar zamani; wajen bunƙasa kiyo da ci gaban tattalin arziƙi.
Ya ce taron zai maida hankali wajen magance matsalolin da sana’ar kiyo ke fuskanta a Nijeriya inda mahalarta taron Dubu Shidda za su wasa ƙwaƙwalwa wajen samar da mafita ga matsalar.
Ajayi ya ce annobar cutar Covid-19 da rashin bada tallafin da ya dace ya jefa ɓangaren sana’ar kiwo cikin mawuyacin hali, duk da irin masana kimiyar Dabbobi da ake da su, waɗanda suka samu horo a ƙasar, sai dai ya ce duk da haka darajar sana’ar kiyo a yanzu haka ta kai ga yadda za ta iya samar wa ƙasar kuɗin da suka kai Naira Tiriliyon Goma sha Ukku.
