Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo ya fice daga jam’iyya PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Sanata Abbo ya sanar da ficewar tasa ne a wata wasika da ya aike wa majalisar dattawa a Larabar nan.
A cikin wasikar dai, Mista Abbo ya bayyana cewa ya yanke shawarar sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ne saboda rashin kyakkyawan shugabanci da PDP ke samu a jihar karkashin gwamna Umaru Fintiri.
