Home Labarai Sanusi ya samu tarbon Kwankwaso, Dambazau a Lagos

Sanusi ya samu tarbon Kwankwaso, Dambazau a Lagos

79
0

A daren jiya Juma’a ne tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya isa Birnin Lagos daga Abuja kan wani karamin jirgin sama.

Idan dai za a iya tunawa a da safiyar jiya Juma’a ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja karkashin jagorancin mai shari’a Anwuli Chikere ta bada umarnin a saki tsohon sarkin daga tsare shin da aka yi a garin Awe na jihar Nasarawa.

Kuma a ranar ne gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya jagoranci dauko sarkin daga Awe zuwa Abuja, bayan ya jagoranci sallar Juma’a a garin na Awe.

Sanusi wanda ya isa filin jirgin Murtala Muhammad na Lagos da misalin karfe 10:15pm na dare ya samu tarbo daga manyan mutane da suka hada da tsohon ministan sufurin sama Osita Chidoka, da tsohon ministan cikin gida Abdulrahman Dambazau, da tsohon gwamnan Kano Rabi’u kwankwaso.

Haka zalika akwai mata, ‘ya’yan sa da sauran ‘yan uwa da abokan arziki da suka je filin jirgin domin tarbon sa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply