Home Labarai Sanusi zai maka Ganduje kotu

Sanusi zai maka Ganduje kotu

73
0

Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya yi barazanar kalubalantar sauya masa gari da aka yi a kotu.

Da yake magana ta hannun lauyan sa Abubakar Balarabe Mahmoud SAN, tsohon sarkin ya ce ba a zo mashi da takardar kamu ba kafin jami’an tsaro su fitar da shi daga fadar sa a ranar Litinin.

Da yake magana da ‘yan jarida ranar Talata a Kano, Mahmoud ya ce tawagar lauyoyin Sanusin za su kalubalanci wannan mataki a kotu.

Ya ce dokar masarautar Kano ta shekarar 2019 bata ba bangaren zartarwa ko wace irin dam aba ta raba sarkin da garin sa.

Ya kara da ce sauke sarkin da dauke daga garin karya hakkin sa ne a matsayin sa na dan adam.

Ya kuma yi kira ga babban sufeton ‘yan sandan kasar, da babban daraktan hukumar tsaro ta DSS su tabbatar da an saki sarkin cikin gaggawa.

A ranar Litinin ne dai gwamnatin Kano ta sauke sarkin saboda rashin girmama ofishin gwamnan jihar da sauran hukumomin jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Usman Alhaji da ya bayyana tsigewar, ya ce ta fara aiki ne nan take.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply