Daga Nuruddeen Ishaqbanye
Wani babban jam’in kiwon lafiya a asibitin kula da cizon maciji na Kaltungo da ke jihar Gomben Nijeriya, Dr Anthony Mohammed, ya gargaɗi waɗanda maciji ya sara, da su guji yin amfani da magungunan gargajiya.
Da yake zanta da jaridar The Punch, Mohammed ya ce magungunan gargajiya ba su da tasiri wajen magance saran maciji, yana mai cewa sun sha samun waɗanda maciji ya sara suka yi amfani da maganin gargajiya, suna zuwa wajen su neman magani, wani lokaci ma cikin mawuyacin hali.

Jami’in ya ƙara da cewa abun da jama’a ya kamata su yi shi ne, hanzarta zuwa asibiti cikin lokaci, domin ana iya magance matsalar cikin ƙanƙanin lokaci idan har an zo asibiti da wuri, ba tare da mara lafiya ya jigata ba.
Haka kuma ya yi kira ga makiyaya da manoma, da su riƙa sanya rufaffun takalma a lokacin da suke daji don kauce wa saran maciji, sannan su riƙa amfani da gidan sauro mai ɗauke da sinadari.
