Sarkin Daura, Mai Martaba Alhaji Umar Faruk Umar, ya karrama ɗiyar Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, Folashade Tinubu-Ojo, da sarautar gargajiya ta ‘Jakadiyar Ƙasar Hausa’.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Folashade Tinubu-Ojo, ta samu sarautar ne a wani biki da aka gudanar a fadar Sarkin Daura.
A yayin bikin, Sarkin Daura ya kuma karrama Ministar Al’adu a gwamnatin Tinubu, Hannatu Musa Musawa, inda ya naɗa ta sarautar ‘Mairamar Ƙasar Hausa’.
An gudanar da bikin cikin al’ada da alfarma a fadar Sarkin Daura, jim kaɗan bayan gudanar da bikin Hawan Magajiya, wanda aka fi sani da Sallar Gani.
Bikin ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, ’yan siyasa da sauran manyan baƙi, ciki har da mata masu riƙe da sarautun gargajiya.
An ce an ba wa Folashade Tinubu-Ojo da Hannatu Musawa sarautun ne bisa la’akari da gudummawar da suke bayarwa ga al’umma, musamman wajen inganta al’adu, ƙarfafa mata da tallafa wa ci gaban al’umma.
Bikin ya kuma kasance wata dama ta nuna muhimmancin masarautar Daura wajen karewa da bunƙasa al’adun Hausawa da kuma karrama mutanen da suka taka rawa wajen ci gaban al’umma.
Haka kuma, taron ya sake bayyana ɗimbin al’adun gargajiya na Daura, inda manyan baki suka haɗu da masarautar wajen bikin karrama waɗannan fitattun mata.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya halarci bikin tare da sauran manyan baƙi da muƙarraban gwamnatinsa.
Naɗa waɗannan sarautu ya ƙara jaddada rawar da masarautun gargajiya ke takawa wajen girmama mutane da kuma ci gaba da raya al’adun Hausawa.
