Home Labarai Sarkin Katsina ya umarci hakimai da su kafa kwamitocin tsaro a yankunansu

Sarkin Katsina ya umarci hakimai da su kafa kwamitocin tsaro a yankunansu

100
0

Matsalar tsaro: MASARAUTAR KATSINA TA BA HAKIMAI UMARNI

Mai martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya umarci hakimai 45 da ke karkashin masarautar sa da su kafa kwamitocin tsaro, a wani mataki na magance matsalar tsaro a yankin.
Sarkin ya bada wannan umarni ne a lokacin wata ganawa da ya yi da hakiman sa a ranar Talatar nan.
Abdulmumini ya umarci hakiman da su yi aiki da sauran dagattan su wajen samar da bayanai ga jami’an tsaron da ke yankunan su da kuma dukkan wani taimako da suke bukata na gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.
Sarkin ya bada tabbacin masarautar sa za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da magance dukkan matsalolin da jihar ta Katsina ke fuskanta.

Ko ta yaya kuke ganin wannan yinƙuri zai taimakawa ƙoƙarin da ake na magance matsalar tsaro a yankin masarautar Katsina?

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply