Home Labarai Sarkin Zazzau ya kara daga darajar Mannir Jaafaru, ya nada sabon Iyan...

Sarkin Zazzau ya kara daga darajar Mannir Jaafaru, ya nada sabon Iyan Zazzau

278
0

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu-Bamalli ya daukaka Yariman Zazzau  Alhaji Mannir Jaafaru zuwa sarautar  Madakin Zazzau, mukamin sarauta mafi girma a masarautar ta Zazzau.

 

Munnir Jaafaru, wanda mahaifinsa Sarki Jaafaru Dan Isyaku ya yi sarautar Zazzau  tsakanin shekarar 1937 zuwa 1959, na daya daga cikin abokan takarar da suka yi neman sarautar Zazzau bayan rasuwar Sarki Alhaji Shehu Idris a watan Satumbar shekarar 2020 acewar jaridar Daly Nigerian.

 

DCL Hausa ta samu labarin cewa  nadin na Mannir Jaafaru a matsayin Madakin Zazzau wani kokari ne da sabon Sarki ke yi na “dinke baraka tare da neman hadin kan masu rike da mukamai a masarautar.

Bayan haka kuma sanarwra da masarautar Zazzau din ta fitar na nuni da cewa an nada dan majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Zaria Abbas Tajjuddeen a matsayin sabon Iyan Zazzau bayan rasuwar da tsohon Iyan Zazzau din ya yi a makon da ya gabata.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply