Home Labarai Sarkin Zazzau zai sauya fasalin masarautarsa

Sarkin Zazzau zai sauya fasalin masarautarsa

193
0

Majalisar masarautar Zazzau ta ce nan ba da dadewa ba zata aikewa gwamnatin jihar Kaduna bukatar sake fasalta masarautar don inganta ayyukanta.

Mai martaba sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu-Bamalli ne ya bayyana haka yayin da mataimakiyar gwamnan jihar Dr Hadiza Balarabe ta jagoranci tawagar jami’an gwamnatin jihar don kai ziyarar girmamawa a fadar ta Zazzau.

Mai martaba sarkin ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta sake yin nazarin ayyukan masarautun da ke fadin jihar ta yadda za ta kara inganta su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply