Home Coronavirus Saudiya ta haramta shafar Ka’abah ga mahajjata

Saudiya ta haramta shafar Ka’abah ga mahajjata

155
0

Kasar Saudiya ta zayyana wasu ka’idojin kariya akan cutar corona ga mahajjatan da aka sahalewa su gudanar da aikin hajin bana.

Daga cikin sabbin dokokin da kasar ta gindaya sun hada da haramtawa mahajjata taba ka’abah ya yin da suke gabatar da aikin hajji.

An kuma bukaci mahajjatan da su rika ba da tazara ta mita daya da rabi domin kauce wa bazuwar annobar Corona.

A karshe kasar ta Saudiya ta bayyana cewa sanya takunkumi ya zama dole ga duk mahajjatan da za su gudanar da wannan ibada a bana.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply