Saudiyya ta samu mutum 3,369 da suka kamu da #coronavirus a rana daya. Jaridar Arab News ta kasar ta ce wannan shi ne adadi mafi yawa da aka taba samu a rana guda. Kawo yanzu cutar ta kama mutum sama da 100,000.
Coronavirus dai ta sa Saudiyya rufe masallatai a watan Maris, sai dai hakan bai tsayar da bazuwar cutar ba.
Ya kuke ganin aikin hajji zai kasance a wannan shekarar?
