Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Saudiyya ta ƙara harajin VAT daga 5% zuwa 15%

Saudiyya ta ƙara harajin VAT daga 5% zuwa 15%

267
0

Gwamnatin Saudiyya ta kara harajin darajar kaya watau VAT daga kashi 5% zuwa kashi 15%.

A cewar kamfanin dillancin labaran kasar, gwamnati za ta dakatar da kudaden alawus na tallafin rayuwa da take ba jama’ar kasar daga ranar 1 ga watan Mayu.

Ministan kudin Saudiyya, kuma mukaddashin ministan tattalin arziki da tsare-tsare Mohammad Aljadaan, ya fada a yau Litinin cewa daukar wannan mataki ya zama wajibi domin magance matsalolin tattalin arziki da cutar coronavirus ta haddasa, ta hanyar da ta dace.

A watan Janairun shekarar 2018 ne dai gwamnatin Saudiyya ta kirkiro da VAT domin inganta hanyoyin samar da kudaden shiga ba ta hanyar mai ba, tun bayan faduwar farashin man a shekarar 2015.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply